Koyon Java Programming Language Dalla Dalla 2019TSARIN JAVA PROGRAMMING

(Structure of Java)


            A cikin darasin da ya gabata, mun dan yi waiwaye ne kadan, a inda muka yi Magana akan yadda ya kamata tunaninka ya kasance a matsayinka na Programmer. Mun kawo wasu halaye da ya kamata a ce ka kwaikwaya domin zama cikakken Programmer. A cikin wannan darasin kuma, za mu juyo a kan Java programming ne, a inda zamu yi Magana akan tsarin yadda ake rubuta java, wato Structure of Java Programmig Language.

            Za’a iya kassafa bagarorin da Java program (da ma sauran programming) suka  kunsa ya zuwa gida biyu: wato Class da kuma Methodko procedure.

           

Class

                Shi class shine kamar madauki ko kuma container na Java program baki dayansa.  Shi class yana dauke ne da  program ko kuma code wanda zaya aiwatar da wani aiki na musamman. Kamar yadda muka fada a darasin da ya gabata, duk wani aikin da ake bukatar computer da ta aiwatar ana rarraba shi ne ya zuwa kananun aiyuka. Ko wane karamin aiki za’a iya amfani da Class wajen bayyana ma computer hanyar da zata bi domin aiwatar da shi.
           

            Method/Procedure


            Shi kuma method, ko kuma function sun kunshi ainahin aikin da class ke yi. Duk inda ka ga method ko kuma function a cikin Programming to zaka iske cewa ya zo ne a cikin wani class.


Structure


            Ga structure din Java programming kamar haka:

public class Gabatarwa{
        public static void main(String [ ] args) {

//code da zaya bayyana aikin da ake bukatan aiwatarwa
}
}
( a kula sosai wanda aka fara budewa shine ake rufewa daga karshe)

     

                                  Fashin Baki


1.     public class Gabatarwa
            Wannan shine a layin farko na structure din Java. Wannan layi shine ke nuna sunan class. Wannan layi yana nuna cewa sunan class dinmuGabatarwa. Idan kuma kun kula, zaku ga cewa shi wannan class shine ke dauke da duk wani abu da za’a rubuta,  a inda ya fara ko kuma ya bude  dacurly bracket ( ),  kuma a karshe ya rufe da shi ( } ).


2.     public static void main(String [ ] args)
Wannan layi na biyu shine ake kira da main method, wato ita ce method din da ke dauke da duk wasu bayanai da computer ke bukata domin fahimtar code din da aka rubuta a ciki (wato aikin da aka bata). Program na Java ba zai taba ronawa ba a saman computer in har babumain method a cikinsa.

3.      // code da zaya bayyana aikin da ake bukata aiwatarwa

Shi kuma wannna rubutu shi ake kira da comment, wato wani Karin bayani ne da programmer zaya iya yi akan code din da ya rubuta, ko kuma wani abu da ake bukata sanyawa a wajen, ta yadda ko da wani ya gani zaya fahimci abin da ake nufi a wurin. Duk a lokacin da computer ta iske “//” a farkon layi to zata tsallake shi ne, saboda ta san baya daga cikin code din.

            Kawo yanzu, muna fatar kowa ya fahimci yadda tsari ko kuma structure na Java yake, kuma ya zamto zaku iya rubuta shi da kanku. Idan mutum ya san bai fahimta ba da yadda  strucuture din take, ko kuma baya iya rubuta shi da kanshi, to muna bashi shawara da ya sake karanta wannan darasi, domin wannan darasi shine kusan gadon bayan wannan kwas din gaba dayansa.

Koyon Java Programming Dalla Dalla Darasi Na Farko 2019GABATARWA


 Muna fatar koya muku yadda ake rubuta program a java, dokokin rubuta java da kuma hanyar da zu kabi  domin zama programmer. Muna fatar zuwa karshen wannan aji (tsawon sati/mako 4) duk wani dalibin da ke a wannan class zaya iya rubuta da kuma runner program a Java.

                             TARIHIN JAVA PROGRAMMING

       

    Wani kamfani da ake kira da Sun Microsystem ne ya fito da programming language na Java sama da shekaru 25 da suka wuce. Tun shigowarsa, Java ya zama programming language da yafi ko wane programming language farin jini. Wannan samun farin jini na Java baya rasa nasaba da irin yadda aka tsara shi ta yadda aka yi amfani da tsofaffin Programming languages masu farin jini a wancan lokacin wajen tsara shi Java din. Bayan haka kuma java shine kadai programming language a wancan lokacin wanda zaka runer shi a kowace compute, sabanin sauran programming languages a wancan lokacin inda computer din da kayi amfani da ita wajen programming din, da ita ce kawai zaka iya runner program din. Bayan haka kuma, Java shine programming din da ake amfani da shi wajen yin softwares da ke aiki akan kananun ababen amfani kamar 

wayar hannu, agogo, TV, radio, Video player, Music Player, electronics da dai sauran ababen amfanin gida.

            Har ya zuwa wannan lokaci, Java shine programming language wanda ya fi ko wane programming language farin jini da kuma samin karbuwa a duniya baki daya. Wayoyin hannu irin su Android, Blackberry da sauransu duk akan yi amfani da Java domin hada Application nasu. Mafin yawancin motocin da zaku ji ance ana programming dinsu da Java ne ake amfani wajen yin hakan.Wadannan sune darussan da muke fatan gabatarwa a tsawon lokacin da zamu dauka a wannan aji.  Da fatan kowa zaya maida hankali domin cimma manufa.
Domin yin programming na java a cikin wayarka ta Android, akwai wani Application da ake kira AIDE for Java, wanda zaka iya saminsa a Google Play Store. Kayi kokarin downloading dinsa indai kasan baka da computer.
Idan kana da computer kuma to akwai Softwares irinsu Eclipse da kuma Netbeans wadanda ake amfani da su wajen rubuta da kuma runner java program.

MENENE PROGRAMMING
            A cikin al’umma ko kuma mutanen dake duniya baki daya , zaka samu al’ummu daban-daban. Ko wace al’umma tana da hanyar da take amfani da ita domin Sadarwa tsakankininsu. Akwai yaruka daban-daban, wanda yawansu baya kirguwa, da al’ummu daban-daban ke amafani da su domin yin mu’amala ta yau da kullum tsakaninsu.

            Abin lura anan dai shine, duk da cewa dukkan harsunan da mutane ke amfani dasu mabam-banta ne, zaka samu ma’anonin sakonnin da ake son isarwa duka iri daya ne. Misali, yadda za kace “tafi gona” da harshen Hausa, ya bam-banta da yadda za ka fada da harshen Turanci, Larabci, Fulatanci, Yarbanci da dai sauransu. Amma kuma za kaga cewa duk ma’anar aikin da ake son a aiwatar ko kuma sakon da ake son isarwa duk daya ne.

            Daga cikin Yarukan da mutane ke amfani da su, idan muka yi duba zamu ga cewa akwai wadanda kwata-kwata basu kamanceceniya tsakainisu (misali Hausa da Faransanci), akwai kuma wadanda za kaga suna kama tsakaninsu sosai (misali Hausa da Fulatanci, Larabci da Kibdanci, ko kuma English da Faransanci). Kai akwai ma Yarukan da tarihi ya nuna cewa daga wasu yarukan aka kirkiro su (misali an kirkiro Turanci daga Faransanci).

            Ba komai yasa muka shiga wannan gona ta masana ilimin harshe ba, sai don mu nuna muku irin yadda yaren computer ko kuma programming language yake da kamanceceniya irin ta yarukan mutane, da kuma yadda computer ke bin irin salon da mutane ke afani da shi wajen aikata wani aiki.

            

            Programming Language shine “Yaren”  da ake amafani da shi waje baiwa computer umarni don ta aikata wani abu.

            Kamar yadda mutane ke amfani da harsunansu wajen bada umarni da kuma bayyana yadda abu yake, haka ake amfani da programming language wajen baiwa computer umarnin yin wani abu ko kuma bayyanam ma computer yadda wani abu yake, ta yadda zata iya amfani da wannan abun a duk lokacin da bukatrasa ta taso.

            Misali, idan za ka yi ma mutum kwatance na wani wuri da yake nema, dole ne ka bayyana masa hanyar da zaya bi daga farko, sana kuma idan ya iske hanyoyi a gabansa wace ce zaya bi daga cikinsu wacce za ta kai shi zuwa wurin da yake nema. Haka idan kana bukatar dafa abinci dole ne ka bi steps din da ake bukata tun daga  wanke tukunya, dorata  saman wuta, har ya zuwa sauke abincin idan ya dafu.

            Ita ma computer haka abin yake wajenta. Dole ne idan kana son computer ta yi maka wani aiki, sai ka bayyana mata yadda aikin yake, da kuma hanyar da zata bi domin yin wannan aiki. Ita kuma za ta dubi wadannan bayanai da ka bata, sai ta soma aiwatar da su daya bayan daya har sai ta kammalasu baki daya sannan ta bayyana maka (idan ka bukaci hakan) sakamakon wannan aiki da ta aikata maka.

            Misali, idan kana bukatar computer ta hada ko kuma ta tara maka wasu lambobi guda uku tare da bayyana maka sakamakon tarawar,  yadda zaka iya bayyana ma computer hanyar da zata bi domin yi maka wannan aiki shine kamar haka:
1.     Dauki lamba ta farko
2.     Dauki lamba ta biyu
3.     Dauki lambar ta ukku
4.     Hada/tara lamba ta daya da biyu da kuma ta ukku
5.     Nuna sakamakon tarawar

Idan computer ta iske wadannan steps, zata bisu ne daya bayan daya daga step na farko har ya zuwa na karshe. Hanyar da ake bi domin bayyana ma computer yadda za ta yi ta aikata wani aiki shi ake kira da Algorithm.

Yadda Zaka Hada Download Site A Blogger Cikin Sauki
Yadda zaka hada Download site a shafinka na Blogger cikin sauki.
Assalamu alaikum A yau insha Allah darasin namu zaiyi duba ne gameda Download Site a shafin blogger/Blogspot

Yadda Ake Saita Blogger Sitemap Da Post Indexing Cikin Sauki


Sanin Kowane Blogspot hosting ne mallakar kamfanin Google wanda suke bada damar bude BLOG domin yin rubutu a kan internet wato Blogging.
Dalilin haka yasa basu bada damar Dora files ba, kamar na sauran website dine irinsu WORDPRESS AUTOINDEX da dai sauransu.
To amma insha Allah a Yau nazo muku da hanya mafi saukin yadda zaka hada download Site A blogspot.
A wannan darasin zamu hada site ne kamar 9jaflaver

Download Current Entclass Blogger Template For Free

TEMPL

Dafarko shiga nan domin ganinbirin site da zamu hada SHIGA NAN
1. Shiga nan kayi create na BLOGGER Blog naka Blogger.Com in kuma ka riga ka bude Blogger to jeka mataki na Biyu

Abubuwa 3 Da Zakayi Bayan Ka Gama Rubuta Blog Post


2.Saika dora wannan template kayi download nashi anan Download 9jaflaver

Bayan kayi download sai kayi upload nashi a shafinka na blogger daga nan sai yadda ake dora file

YADDA AKE DORA FILE A BLOGGER
Ga yadda ake dora file a bligspot da farko ka sauke wannan app din mai suna URL SHORTENER gashi a kasa

URL SHORTENER

Yadda zakayi shine idan ka samo URL na wakar da kakeson upload Saika sakashi a URL SHORTENER zai chanza maka link din daga nan saikazo blogger naka ka saka shi
Shiga ka saka link naka da sunan link misali DOWNLOAD acikin post din shikenan idan anyi download direct zaiyi download ba tareda Coyright ba saidai dole kayi description da yewa domin samun ADSENSES

Yadda Zakayi Unblock Na Domain Naka A Facebook Ta Hanyar DebuggerAssalamu alaikum barka da zuwa freenet shafin koyarda Kimiyyabda fasahar zamani cikin harshen hausa tare da ma rubuci Usman ict
A yau insha Allah Darasin namu zaiyi duba ne izuwaga Yadda zakayi  unblock na domain naka wanda facebook sukayi block nashi.

Yadda Ake Saita Auto Gmail Signature Cikin Sauki 2019


Sanin kowa ne facebook ta zama babbar kafa ta sada zumunta wanda wannan shi yake ba Bloggers damar cin karen su ba babbaga ta hanyar sharing na post i zuwa shafin na facebook.
Wannan darasin mun gwada shi yana aiki 100%
Domin kuwa mun bude domain kusan 3 dashi wannan gwaji ne muka yi domin bude naka saika bi wadannan matakan:-

Yadda Zaka Sayi 1GB Akan N200 Da 4GB Akan N1000 A Layin Airtel


YADDA ZAKAYI UNBLOCK NA URL NAKA A FACEBOOK

1.Dafarko ka shiga wannan link din na kasa
Facebook Sharing Debugger


 2.Saika danna Debug Daga nan zai kaika wani page wanda zaka ga warning kamar haka:-


Yadda Ake Neman Keyword Ta Hanyar Amfani Da Soovle Cikin Sauki
3. Saika danna "Let Us Know daga nan zai kaika inda zaka rubuta comaplain naka


Kawai ka Copy wannan Sakon kayi paste a box dina ka tabbata ka canza
SUNANA
DA
SUNAN WEBSITE DIN WATO URL DINKA
daga nan saika danna SEND


Good Morning Facebook!
With due respect, I would like to inform you my website URL have been blocked on Facebook. Recently I got know my website URL:https://www.yourwebsitenamehere.com has blocked on Facebook and prohibited me to share my website links over my pages and my timeline.
I didn’t go against your policies. I apologize If I have broken any Facebook policy by any mistake.
It is requested please unblock my website URL and enable its links. I thank Facebook Team for making it a safe place for all.!
Please Unblock my website.
URL:  https://www.sunanshafinka.com
Thanks in Advanced.
Usman ictSaika jira 24 Hours Insha Allah URL naka zai zama Unblock Allah ya bada Sa, a 
Daga freenet
Note:- wannan aikin da Chrome Browser zakayi

Yadda Ake Saita Blogger Sitemap Da Post Indexing Cikin Sauki
Barka da zuwa shafin freenet Wannan shafi ne da yake taimaka wa yan arewa musamman a fannin kimiya da fasha muna gabatar da darusa iri iri anan. 
A yau insha Allah zamuyi darasi ne gameda Sitemap na Blogger wato Blogspot. 

Yadda Ake Saita Auto Gmail Signature Cikin Sauki 2019


Dafarko menene sitemap? 
Sitemap wata fasaha ce wadda take ba Search Engine damar Daukar Abinda kakeso su dauka a Shafinka wato shine zaiba crawler damat Locating na Content na blogger nakan. 
Wannan shine takai taccen Aikin site map. 
Shin Dole ne saina saita Sitemap? 
Sai ince maka EH sannan ince maka A A 
Sitemap ba dole bane amma site map shine zai sau kakewa Crawler Idan ta shigo Blog naka ta dauki abinda ta ke So,  
Agaskiya yana da kyau ka saita Sitemap a Blog naka saboda samun Good SEARCH ENGINES OPTIMIZATION  (SEO) 
Wannan shine. 

Yadda Ake Neman Keyword Ta Hanyar Amfani Da Soovle Cikin Sauki


Yadda ake saita SITEMAP domin saita Sitemap saika bi wadannan matakan kamar haka:-

Yadda Zaka Sayi 1GB Akan N200 Da 4GB Akan N1000 A Layin Airtel


Dafarko shiga wannan link din domin Generating Na sitemap shiga
Bayan ya bude saika rubuta Full Blog Address naka kamar yadda kake gani a hoton nan
Misali:-
http//www.freenet.com.ng
Saika dannan Generate

Saika COPY wannan code din da suka baka 

Sai kaje Blogger naka domin Extracting na Code din


Shiga SETTING shiga SEARCH PREFERENCE  shiga CUSTOM ROBOTS. txtSaikayi enable nashi sannan ka zuba wannan Code din a box nan saikayi Save shikenan. 


Sai kaje 

Settings– > Search Preferences-> Google Search Console 


Shiga menu icon


Shiga sitemap(idan bakayi verifying na Property naka ba to dole kayi verifying tukunna


Sannan ka rubuta site map Adress naka misali
(http://freenet.com.ng/sitemap.xml
Shikenan ka danna submitShikenan congrat


Yadda zakayi cheecking na Site map naka sai kaje OPERA ko BROWSER naka sannan ka rubuta Address na site map naka misali


freenet.com.ng/sitemap.xml

Saikayi search zaka ga result kamar yadda kuke gani a wannan hoton


 to shikenan ka gama saita sitemap naka amma in kaga error to bai saitu ba sai kayi Comment da matsalar ka
Mun gode naku Usman Ict freenet


Yadda Ake Saita Auto Gmail Signature Cikin Sauki 2019A yau Darasin namu zaiyi duba ne gameda Abinda ya shafi GMAIL. 
Menene gmail,  Gmail yana nufin Google Mail Wato wani akwatin sako ne wanda yake running akan Yanar gizo wanda zai baka damar Turawa da Karban Sako a kan yanar gizo gizo. 

Yadda Zaka Sayi 1GB Akan N200 Da 4GB Akan N1000 A Layin Airtel


Gmail Shine mail mafi shahara sannan Shine Gmail mafi tsaro A duniya. 
Saboda Gmail yana nan kamar master mail ne saboda yana aiki a gurare da dama saboda kuwa yana Karkashin Babban Kamfani wato GOOGLE INC.


Yadda Ake Neman Keyword Ta Hanyar Amfani Da Soovle Cikin Sauki


Menene Gmail signature:- Gmail signature wato wani Signing ne wanda shi zai wakilci sakonnninka wanda shi zai nuna cewa lallai wannan sakon ya fito ne daga waine.. 
Atakaice da Gmail Signature shine Sa Hannunka na Gmail naka wannan shine kawai

Yadda ake saita Gmail signature ba tareda bata lokaci ba ku bi wadannan matakan domin saita Gmail Auto Signature naku 

Dafarko ka shiga Gamail Account naka saika danna Menu Icon kamar yadda kake gani a wannan hotin


Daga nan saika shiga SETTING kamar yaddabkake gani a wannan hoton

Saika zabi gmail da kake son saita mishi wannan signature din 
Daga nan saika shiga MOBILE SIGNATURE 

To yanzu saika rubutu signature naka wato wanda zaibwakilci sa hannunka na sakonninka na gmail

Saika danna OK shikenan kayi nasarar saita AUTO GMAIL SIGNATURE naka 
Duk sakon da ka tura zaije da Signature naka 

Yadda Zaka Sayi 1GB Akan N200 Da 4GB Akan N1000 A Layin Airtel
Assalamu alaikum Barkanku da war haka da fatan kowa yana lafiya ayau insha Allah zan nuna muku yadda zaku sayi Airtel Data Bundle akan farashi mai sauki.
Sanin kowa ne DATA/MB shine abu mafi sauyuwa ga masu wayoyin Android

Abubuwa 3 Da Zakayi Bayan Ka Gama Rubuta Blog Post


Saboda tsadar da Data yayi hakan yana hana wasu mutane hatta aiki da Social media.
Sabo da haka zaka ga mutane da dama suna Neman data maibsaukin kudi to insha Allah yau Anzo gurin.
Wannan Garabasar na Masu aiki da layin AIRTEL ne kawai sannan kuma wannan tsarin gaskiya SA, A ne saboda haka ba kowani layi yake yi ba.

Yadda Ake Neman Keyword Ta Hanyar Amfani Da Soovle Cikin Sauki


Ga yadda data din yake:-

  1. N100/200MB/DAILY
  2. N200/1GB/7DAYS
  3. N500/2GB/14DAYS
  4. N1000/4GB/MNTLY
  5. N1500/6G/7DAYS

Wannan shine farashin wannan data din. 

Ba tareda bata lokaci ba Saiku bi wadannan matakan domin sayan Data
1. Da farko Dannan *141*241#2. Saikayi reply da MB da kake son saya

Sai kayi Replya da 1 domin confirm na sayan data plan din


Shikenan Kayi nasarar sayan data Plan naka
Idan kaga ya nuna maka
"YOU ARE NOT ELIGIBLE" to sim naka bazaiyi ba
Amma idan ya nuna maka "insufficient" To ka saka CARD kawai naka zai saya.
Wato ina nufin ko babu kudi a sim naka zaka iya sayan wannan Data din.

Na tabbatar zakuji dadin wannan Data plan din sosai wallahi saboda yana Lasting sosai
Daga Freenet.com.ng

Download Current Entclass Blogger Template For Free


After a long break we are again sharing a fascinating SEO Friendly, Responsive and Ads Ready Entclass Blogger Template. Hopefully the features of this template will be able to meet all your blogging needs. Despite the desire to engage in work, I have been avoiding blogging for a long time. Hopefully from now on I can give regular time to everyone.

Search engine optimization
All parts of this template have been created to fit the search engine perfectly. If you use it, no part of the template should be thought of as SEO.
Available Dark Mode:
Responsive Design
Built to suit all of the most widely used small devices of today. For this, the template can be easily read from the computer, laptop, tablet and mobile. Highly Mobile Optimized, especially for mobile to slow internet users to visit easily. Moreover, all of its widgets are designed separately to suit all types of devices.
Ads Ready
Those who use different types of blogs or are planning to use them in the future, can enjoy the special benefits of using this template. Because the layout of the template has been scaled to accommodate the ad code in various places.
Fast speed
An important feature of this template is that it will load very fast in all types of browsers. Because it uses Minify, all types of code including HTML5, CSS3, JavaScript. As a result, it does not have much effect on your blog's load time.
There are also many other features that we are not describing here. When you view the live demo of the template, you can get full ideas.
 DEMO      DOWNLOAD

Yadda Ake Neman Keyword Ta Hanyar Amfani Da Soovle Cikin Sauki
A yau zamuyi duba ne gameda Keyword agaskiya Keyword shine abu mafi amfani wurin rubuta post
wannan ne yasa a yau zanyi kokarin nuna muku yadda keyword suke da yadda ake nemo su a wannan darasi, saboda keyword shine abunda zaisa Post naka ya rika samun views ta SEARCH ENGINES saboda kuwa indai kana rubuta post wanda babu keyword aciki to fa ba wanda zai budo post din ta google saboda bakasan menene mutane suke nema a google ba to gaskiya ba yadda zaka iya tacking na visitors.

Saboda kuwa duk wani post da zaka rubuta idan baida alaka da abunda mutane ke nema a Search Engine to bazaka samu Traffic ta Search Engine ba.

Read More › › Abubuwa 3 Da Zakayi Bayan Ka Gama Rubuta Blog Post

Wannan Yasa nakeso in nuna muku best KEYWORD RESEARCHER wato wannan wani shafi ne wanda zai baka damar samun keyword wanda zaka gina post naka saboda Kasamu ranking a google.

Ga misalan keyword kamar haka idan kuka duba wannan hoton zakuga inda na kewaye da red pain to wadannan sune keyword


Wadannan sune keyword wato abubuwanda mutane ke nema a Google da sauran search enginesDa farko ka shiga wannan shafin:-

www.Soovle.com

Zakaga Textbox saika sanya keyword naka wato abinda kake so ka rubuta post akansa zakaga suggesstion diyewa saika nemi keywords masu kyau.Wannan shine maanar keyword

Abubuwa 3 Da Zakayi Bayan Ka Gama Rubuta Blog Post
Barka zuwa shafin Freenet.com.ng Yau Daransin Namu zamuyi magana ne gameda abubuwanda ya kamata mutum yayi bayan yayi Post a Shafinsa na Blogger ko wordpress.
Wasu sun dauka cewa da zaran ka gama rubuta post kawai saika dauke shi ka kaishi facebook ko whtasapp ko twitter kana sharing, Sharin na Post yanada kyau sosai to amma Duk wani Traffic da zaka samu muddin Traffic din yana fitowa ta Social Media ne to a gaskiya har yanzu blog naka yana cikin hatsari sosai saboda haka ne yasa muka bude wannan shafin na Freenet domin inganta SEO na blog namu musamman arewa.
Kar in cikamu da surutu bari muje kai tsaye zuwaga darasin namu zanyi kokarin hasaso mana wasu abubuwanda insha Allah idan kayi so to zakaga POst naka yana INDEXING a google bin da Yahoo ngasu kamar haka:-
           

TABLE OF CONTENTS


  1. Karanta abunda ka rubuta
  2. Hada Backlinks 
  3. Sharing na post naka 


1.KARANTA  DARASIN DA KA RUBUTA

Anaso idan mutum yagama rubuta post ya tabbat ya karance shi duka kafin google ya fara indexing na post naka saboda karanta post din zai taimaka a wurare kamar haka, zaka gera wrong speling,zaka saka Heading da Subheading, zaka tsara rubutunka da poin masu kyau

Read more › › Yadda Ake Neman Keyword Ta Hanyar Amfani Da Soovle Cikin Sauki

 2.HADA BACKLINKS

A gaskiya backlinks sunada matukar amfani sosai musamman idan CRAWLER ta shigo shafinka, Idan ka saka backlinks a post naka  to idan crawler tazo daukan post din saitaga wani LINK na wani post din to saita dauka dashi duka sannan zata kara RANKING Naka a google sosai kuma BACKLINKS suna taimakon mai karatu yayi Tsalle daga Post da yake karantawa zuwa wani post din wanda kuwa kaga inda ace post din kawi zai karanta ya fita to saika ga ya kara tsalle zuwa wani post din zai dade a shafinka sannan zaka samu PAGEVIEWS mai yewa kenan

Ga yadda zaka rika saka backlink naka ka rika connecting na post da post kamar yadda kake gani a wannan hoton

Ka rika saka "Read more a Post naka yana saka google adsense suyi Approve da wuri sannan yana kara SEO speed sosai


3.SHARING NA POST

Sharing na post yanada matukar amfani amma gaskiya bai kamata ka dogara da Social media Traffic ba saboda baida karfi , Amma ba laifi zaka iya sharing na post naka zuwa social media 
domin samun visitors masu yewa